![]() |
Abdoulrahmane Tiani |
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da zaman makoki na kwana uku a kasar bayan ajalin wasu mutane 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da ake zargin “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar Nijar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a.
Ma’aikatar ta ce ‘yan ta’addan sun yi ajalin mutanen ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata.
Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin tare da shan alwashin ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta’addanci a yankin.