![]() |
Wata babbar kotun tarayya da ke Lokoja a ranar Juma’a ta hana hukumar zabe ta kasa INEC karbar takardar korafe-korafe da nufin fara shirin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.
Mai shari’a Isa Dashen, ne ya ba da umarnin bayan karar da aka shigar gabansa.
Masu shigar da kara, Anebe Jacob Ogirma, John Adebosi, Musa Adeiza, Ahmed Usman, da kuma Maleek Yahaya, sun shigar da karar ne ta hannun lauyoyinsu suna neman a hana INEC karbar kudirin kiranyen na matakin da ake shirin dauka kan Sanata Akpoti-Uduaghan, Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya.
Sun nemi kotun da ta umurci INEC da kada ta karbi koke daga wasu da ake zargi da nufin fara shirin yi wa Sanatan kiranyen.
Mai shari’a Isa Dashen ya amince da bukatar kuma ya bayar da umarnin a mika umarnin ga wanda ake kara wato INEC,tare da sanya ranar 6 ga Mayu don ci gaba da sauraron karar kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito.