![]() |
EFCC |
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da mutane hudu a gaban kotu bisa zargin almundahanar miliyan 50 a Borno
A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar ta gurfanar da wasu mutane hudu a gaban mai Shari’a Muhammad Maina na babbar kotun jihar Borno da ke Maiduguri, bisa zargin almundahanar Naira miliyan 50.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar a shafins EFCC na X, an gurfanar da wadanda ake tuhuman da suka hada da Mohammed Nuhu, Babagana Maru, Ahmadu Sale, da kuma Alhaji Mala Gana, bisa zargin cin amana da karkatar da tsabar kudi miliyan hamsin tare da sauran tuhume tuhume.