Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja hadin guiwa da sojoji ta ce ta yi nasarar ceto wani sojin ruwa da karin wasu fararen hula biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Mpape da ke Abuja a ranar 21 ga watan Maris, 2025.
A cikin wata sanarwa da DCL Hausa ta samu kwafi da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josephine Ade, ta ce da yammacin ranar 21 ga watan, wasu mutane dauke da muggan makamai suka hari rukunin gidajen Mamman Vatsa suka tare ababen hawan da ke wucewa a titi, sannan suka bude wuta a harbin kan mai uwa da wabi, suka sace mutane uku.
Ba da jimawa ba, wadannan barayin daji suka kira waya suna neman kudin fansa Naira milyan 500 ga jami’in sojin ruwan da kuma Naira milyan dari bibbiyi daga sauran fararen hular.
Sanarwa ta ce rundunar ‘yan sandan hadin guiwa da sojoji da jami’an tsaron ciki na DSS da ‘yan banga suka shiga farautar wadannan barayin daji bayan samun labarin faruwar hakan a tsaunukan Mpape, Gidan Bawa, Anguwan Mu’azu da Yelwa, inda a nan ne suka yi nasarar ceto mutanen dukansu ba tare da an lahanta su ba.
Kazalika, ‘yan sandan sun samu nasarar kwato kudaden da yawansu ya Kai Naira milyan 3.2 da ake zargin kudin fansa ne.