Dakataccen gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana da alaka da kungiyoyin yan tada kayar baya da suka addabar yankin wajen yunkurin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da sunansa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Nelson Chukwudi ya fitar a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ya ce faifan bidiyon da ake yadawa ake alakanta shi da gwamnan na yadda wasu bata gari ke bata kadarorin gwamnatin tarayya a jihar