Dakatacciyar sanata daga jihar Kogi ta tsakiya Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci al’umma da su yi watsi da wani rahoto da ake yadawa da yake cewa ta nemi afuwar majalisar dattawan Nijeriya.
Wannan dai na a cikin wata sanarwa da yar majalisar ta fitar inda ta bayyana cewa har yanzu tana kan kalaman ta don haka ba wani hakuri da za ta bayar.
Majalisar dattijai ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida a baya bayan nan, bisa zargin aikata ba daidai ba, bayan takun-saka tsakaninta da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.