Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan fasa gidan gyaran halin Koton Karfe da ke jihar Kogi.
Wannan dai na a cikin wata sanarwa da ministan cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan labarai, Babatunde Alao ya fitar a Abuja, wanda ya bayyana lamarin da abin takaici.
Ministan ya kuma umurci mukaddashin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali, Sylvester Ndidi da ya gaggauta fara bincike domin gano musabbabin abin da ya haddasa faruwar lamarin.