Gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya sun maka shugaba Bola Tinubu kotun kolin kasar inda suka kalubalantar ayyana dokar ta baci a jihar Ribas.
Gwamnonin sun hada da gwamnan jihar Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Plateau, da Zamfara, sun ce shugaban kasa ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna da mataimakiyarsa a dimokuradiyyance, inda suka bayyana matakin a matsiyin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu da daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.