Hukumar lafiya ta duniya ce ta bayyana hakan a cikin wani rahoto da BBC News Africa ta fitar.
Rahoton ya ce Nijeriya ce kasar da tafi kowace kasa a nahiyar Afrika masu amfani da man da ke saka hasken fata da kashi 77 cikin dari.
Rahoton ya nuna yadda wasu iyaye ke amfani da ababe da ke da ke sa hasken fata ga yara kanana harma da jarirai.
BBC News Africa ta bayyana jihar Kano na daya daga cikin manyan garuruwa da ake amfani da mayuka bake haska fata a kasar.