Hukumar dake yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati EFCC ta sake gurfanar da tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya.
Kazalika an kuma gurfanar da tsohon shugaban NNPC Aminu Baba-Kusa da wasu kamfanoni biyu Acacia Holdings Limited da Reliance Referral Hospital Limited a gaban wata babbar kotu da ke Abuja.
Tun a shekarar 2015 ne aka fara gurfanar da Sambo Dasuki a gaban kuliya bisa zargin sa da laifin karkatar da wasu makudan kudade.