![]() |
Tutar Kasar Iran |
Bayan tashi wasa chanjaras biyu da biyu tsakaninta da Uzbekistan a filin wasa na Azadi da ke Tehran a Talatar nan, Iran ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya ta 2026.
Dan wasan Iran da ke taka leda a Intermilan, Mehdi Taremi, ne ya zura kwallaye biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a fafatawar, lamarin da ya baiwa tawagar ta Iran damar shiga gasar karo na hudu a jere, jimulla karo na bakwai a tarihi.
Tawagar Uzbekistan ce ta fara jan ragamar wasan bayan da Dan wasa Khojimat Erkinov ya zura kwallo a minti na 16, sai dai Taremi ya sauya lamarin a minti na 52, yanzu haka dai Iran ita ce ta farko da maki 20 a rukunin A na gasar cancantar shiga gasar cin kofin Duniya a yankin Asia.