![]() |
Shugaban NAHCON tare da ministan lafiya |
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sha alwashin kara inganta shirin kiwon lafiya ga mahajjatan kasar a yayin aikin hajjin 2025 a kasar Saudiyya.
Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate, ya sanar da hakan a lokacin da ya kammala duba kayan aikin kiwon lafiya a sashen Hukumar Kula da aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON a birnin Makkah, Saudiya.
A lokacin ziyarar da ya kai ofishin NAHCON da ke Ummul-Jud a Makkah, Minista Pate ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnati domin magance manyan matsalolin kiwon lafiya da mahajjatan Nijeriya ke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da Muhammad Ahmad Musa, jagoran sashen yada labaran NAHCON ya fitar, hukumar ta shirya aikin hajji a Nijeriya ta ce minista Ali Pate tare da rakiyar manyan jami’an ma’aikatar lafiya, ya gudanar da cikakken bincike kan motocin daukar marasa lafiya na NAHCON, duba kayayyakin likitanci, da kuma tantance shirin kayan aikin asibitocin Nijeriya a Saudiyya.
![]() |
Minista Mohammed Ali Pate tare da shugaban NAHCON Farfesa Saleh Pakistan a Makkah |
Ziyarar ta haskaka muhimman fannoni da ke bukatar ingantawa, ciki har da karin magungunan da ake bukata, rigakafi, kayan aikin likitanci, da kuma motocin daukar marasa lafiya da za su iya aiki yadda ya kamata.
Shugaban hukumar kula da Aikin Hajji ta NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, yana mai jaddada muhimmancinsa musamman ga kula da lafiyar alhazan Nijeriya.