Kungiyar Kwadago a Nijeriya ta yi Allah wadai da kakaba dokar ta baci a jihar Rivers, ta kuma yi barazanar daukar mataki idan har gwamnati ba ta janye dokar ta ɓaci a jihar.
Wannan gargadi ya fito ne daga cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka hada da kungiyar kwadago reshen jihar Rivers Alex Agwanwor da shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Ikechukwu Onyefuru da wasu kungiyoyi suka sanyawa hannu.
A cewar shuwagabannin kungiyoyin al’ummar jihar Rivers sun fito sun zabi wadanda suke so su shugabancesu sabi da haka duk wani yunkuri na dakatar da su, ba tare da bin tsarin mulkin kasa ba yana kawo cikas ga dimokradiyya.