![]() |
Gwamnan jihar Kano |
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan sabuwar ma’aikatar tsaro da lamuran cikin gida Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (Rtd).
Kwamishinan na cikin wadanda suka kama aiki a watan Agusta na 2024 kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Idan ba a manta ba a ranar 05 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025, kwamishinan kula da ingancin ayyuka Mohammed Diggol ya yi murabus daga mukaminsa.