An gurfanar da wata mai gyaran gashi bisa zargin satar katin ATM da naira 80,000 na kwastomarta

-

 

An gurfanar da wata mai gyaran gashi bisa zargin satar katin ATM da naira 80,000 na kwastomarta

Wata mai sana’ar gyaran gashi mai suna Martina Auta ‘yar shekara 30, wacce ake zargi da sace wa  kwastomar ta naira 80,000 da katin ATM guda biyu a ranar Laraba, ta gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Kaduna.

Ita dai wadda ake zargin wacce ke zaune a Narayi a Kaduna, tana fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da cin amana da sata, kuma ta musanta aikata laifin.

Mai gabatar da kara, Sufeta Chidi Leo, ya ce wadda ake kara ta aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Maris a unguwar Barnawa da ke Kaduna da misalin karfe 3:00 na rana.

Leo ya shaidawa kotun cewa wadda ake tuhuma ta sace naira 80,000 da kuma katin ATM guda biyu a cikin jakar hannun Misis Rose Adams, wacce ta zo gyaran gashin kanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara