Hukumar hana yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta bayyana cewa an samu rahoton mutane 886 aka yi zargin sun kamu da cutar kwalara ta kuma halaka mutane 14 a cikin makonni biyar na farko na farkon shekara, tsakanin 27 ga Janairu zuwa 2 ga Fabrairun 2025.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta kara da cewa an samu bullar cutar a jihohi 22 na kasar baki daya.
Rahoton ya nuna karuwar kashi 75 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da kashi 250 na mace-mace idan aka kwatanta da na shekarar 2024.
A cewar NCDC, jihar Bayelsa ce ke da kashi 78 cikin 100 na masu dauke da cutar da mutane 695 da ake zargin sun kamu da ita.
Sauran jihohin da cutar ta bulla sun hada da Rivers 54, Niger 33, da Abia da ke da 32.