![]() |
Alhaji Atiku Abubakar |
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce baya da tabbacin ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira a wani shirin talabijin mai suna Untold Stories da Adesuwa Giwa-Osagie, Daily Trust ta samu.
A kwanakin baya ne tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya sanar da shirin yin ‘merger’ da wasu ‘yan adawa domin tunkarar zaben 2027.
Sai dai bayan bayyana kudurin na su anyi ta cece-kuce kan wanda zai jagoranci hadakar kuma ya zama dan takarar shugaban kasa, inda ake ganin tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cikin manyan jiga-jigai a yayin hadakar.
Da aka tambayi Atiku ko zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, Atiku ya ce bai sani ba, domin da farko dole ne a samar da tsari mai kyau, fiye da kowane lokaci a tarihin siyasar kasar nan, sai dai bai janye yiyuwar tsayawa takarar ba.