Abdullahi Galadanci ya rasu ne a ranar Laraba,26 ga Maris 2025 bayan gajeriyar jinya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhininsa game da wannan rashi, inda ya bayyana Tanka Galadanci a matsayin mutum mai kwazo kuma mai kima a gwamnatinsa bisa irin gudunmawar da ya bayar ga kafafen yada labarai na jihar.
Sanarwar ta ce rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga gwamnati da jihar Kano baki daya.
Gwamnan ya mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwansa, abokansa, da al’ummar jihar Kano baki daya.