Gwamnatin Nijeriya ta fara biyan naira 77,000 alawus na wata-wata ga matasan NYSC
Bayan jinkirin biyan sabon alawus din na naira 77,000, da Shugaba Tinubu ya amince da yin karin watanni shida da suka gabata, a yanzu matasan sun fara ganin sabon alawus din nasu.
A lokutan baya ana biyan masu yi wa kasa hidima alawus na naira 33,000, karin da aka yi tun a shekarar 2020 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daya daga cikin masu yi wa kasa hidima a jihar kano Nkiruk ta shaida wa SolaceBase a ranar Laraba cewa, zuwa yanzu an fara biyan alawus din na naira 77,000 ga masu yi wa kasar hidima.