![]() |
Majalisar wakilai |
Kudurori arba’in da biyu na gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya sun tsallake karatu na biyu a ranar Laraba a majalisar wakilai.
Daga cikin kudurorin har da na cire rigar kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni da mataimakansu, matakin da ake gani zai dakile cin hanci da rashawa, kawar da rashin adalci da kuma kara daukar matakai a ma’aikatun gwamnati.
Wannan ya biyo bayan kudurorin 39 da suka kai matakin karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Talata wanda aka tafka mahawara akai.