![]() |
Sojoji |
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da tura dakarunta 171 zuwa yankin Abyei da ke kan iyakar Sudan ta Kudu domin aikin wanzar da zaman lafiya.
Babban hafsan Sojojin Nijeriya, Manjo-Janar Boniface Sinjen, ya bayyana hakan ne a Jaji Military Cantonment dake Kaduna, lokacin da yake jawabi ne ga sojojin da suka yaye na tawagar Nijeriya ta 3, da za a tura zuwa Abyei karkashin rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (UNISFA).
Ya jaddada muhimmancin aikin, inda ya bayyana cewa, ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba aikin soja ba ne kawai, aiki ne na tabbatar da zaman lafiya, diflomasiyya, da hidima ga al’umma.
Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na da tarihi mai kyau a ayyukan wanzar da zaman lafiya, inda dakarunta ke taka rawar gani wajen maido da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rikici a fadin Afrika da ma duniya baki daya.