Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya ta tabbatar da cewa kungiyoyin siyasa 91 ne suka gabatar da bukatar yi musu rejista a matsayin jam’iyyun siyasa.
Jam’iyyar PDP ta ce wannan ya nuna rashin hadin kai na jam’iyyun adawa, yayin da NNPP ta alakanta shi da rashin iya jagoranci na jam’iyyar APC.
A gefe daya jam’iyyar LP ta yi maraba da wannan lamarin, sai dai jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da hannu a kirkiro wadannan jam’iyyun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.