Litar man fetur da ake shigowa da ita daga ƙasashen waje, wadda ‘yan kasuwa ke saye ₦797 a makon jiya, a yanzu ta kai ₦885 a kowace lita.
An samu ƙarin ₦88 kan kowace litar man fetur cikin mako guda, kamar yadda alkaluman kungiyar ‘yan dillalan mai wato Major Energies Marketers Association of Nigeria suka nuna.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, sabon farashin ya zarce na dilolin matatar Dangote da ₦25, da ke sayar da kowace lita ₦860 ga ‘yan kasuwa, haka kuma ya wuce farashin ₦815 da dillalan ke dauko mai a matatar Dangote.