Kungiyar masu man fetur ta Nijeriya ta tabbatar da cewa matatar man Dangote har yanzu ba ta fara sayar da man fetur da dala ba, duk da yadda ta nuna a baya.
Shugaban kungiyar PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce duk da tattaunawar yiwuwar sayar da man a dala, amma ba a sanar da kungiyar a hukumance ba game da sauye-sauyen sayar da man da aka samu.
Ya ce a iya saninsa, har zuwa yanzu, mambobin kungiyar suna ci gaba da siyan man a Nijeriya da Naira.