Gwamnatin kasar Birtaniya ta fitar da jerin sunayen wasu mutane daga kasashe daban-daban da suka mutu a kasar suka bar kadarori da ba a karba ba, ciki har da ‘yan Nijeriya 58.
A cikin jerin sunayen da aka sabunta a ranar Litinin, 24 ga Maris, gwamnatin Burtaniya ta fitar da cewa adadin mutane 5,806 daga kasashe daban-daban ne suka mutu ba tare da wani ya nemi kadarorinsu ba.
A cikin sunayen da aka fitar akwai bayanan ranar haihuwa, wurin zama da kuma ranar mutuwa.