![]() |
Majalisar wakilai |
Kudurin da ke neman mayar da Nijeriya tsarin mulki mai amfani da ‘Prime Minister’ ya zarce karatu na biyu a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis.
Kudurin na daga cikin kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya guda 31 da aka zartar domin yin karatu na biyu a zauren da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu ya jagoranta a ranar Alhamis.
Kudirin dokar wanda shugaban marasa rinjaye na majalisa Kingsley Chinda da mambobin majalisar 59 suka goyi baya, na kokarin sauya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda akai wa kwaskwarima a shekarar 1999, don samar da ofishin Firaminista a matsayin shugaban gwamnati da ofishin shugaban kasa da kuma samar da tsarin yadda za a gudanar da zabe.