![]() |
Maryam Sulaiman/Uba Sani |
Shugabar matan jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta yi watsi da tafiyar El-rufa’i tare da karbar tafiyar Gwamna Uba Sani
Maryam Suleiman, wadda ta kasance ta hannun daman El-Rufai, ta bayyana cewa komawarsa jam’iyyar SDP, lissafi ne da ba daidai ba.
Shugabar matar wadda a baya aka dakatar da ita daga jam’iyyar saboda kalaman batanci ga Gwamna Uba Sani, ta bayyana nadamar abinda ta aikata.
A yayin wata tattaunawa da manema labarai ta ce ba ta san abubuwan da ke faruwa a lokacin da ta caccaki gwamna Uba Sani ba, amma zuwa yanzu ta gane kuskurenta.