![]() |
Atiku Abubakar |
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar musanta ikirarin da ake na cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bashi tallafin kudi na yakin neman zabe a zaben shugaban kasa da ya gabata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Paul Ibe ya fitar, ofishin yada labarai na Atiku ya karyata rahotannin da ke nuni da cewa Sanwo-Olu, ta hannun Ms. Aisha Achimugu, ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa kudi da ake zargin mallakar jihar Legas ne, abinda ya kira makircin ‘yan siyasa da suka kulla.
A farkon makon da ya gabata ne jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ana binciken Ms Achimugu kan zargin karkatar da kudade da dama.
Hukumar EFCC mai yaki da cin hani da rashawa a Nijeriya na ci gaba da binciken matar da ake zargi.