![]() |
Godswill Akpabio |
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce jam’iyyar APC za ta karbi mulki a jihar Kano a shekarar 2027.
Akpabio ya bayanna haka ne a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya kai ziyara ga mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado.
Ya ce da muhimman ayyukan da Sanata Basheer Lado ke yi a jihar, Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, APC na kara samun nasara a jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu jihar na karkashin jam’iyyar NNPP, inda Abba Kabir Yusuf ke a matsayin gwamna.