![]() |
Usman Ododo |
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu mutane shida na al’ummar Ayetoro-Kiri da ke karamar hukumar Kaba-Bunu ta jihar Kogi.
Jaridar The Guardian ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, inda ‘yan bindigar da ke kan babura suka mamaye yankin.
‘Yan bindigar sun fara kai hari ne a wani shagon sayar da wayoyin tare da kwashe wayoyin hannu sama da 50 inda suka rika harbin bindigogi kai tsaye.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun kama al’ummar garin domin karbar kudin fansa, lamarin da ya haifar da tashin hankali ga al’ummar yankin,bayanai ya sun tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa ba har ya zuwa lokacin hada wannan lokacin.