![]() |
Malam Umar Namadi |
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya bayyana shirin gwamnatinsa na yi wa makiyaya rijista a jihar sakamakon karuwar kwararar makiyaya daga jamhuriyar Nijar zuwa Jigawa
Gwamna Namadi ya bayyana damuwar sa kan yadda ake samun karuwar mace-mace da raunata mutane da rakuma wadanda suka fito daga jamhuriyar Nijar, yayin da suke tsallaka manyan tituna a jihar.
Jihar Jigawa,na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin kasar da ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar, kasar da ta shahara wajen kiwon rakuma, da a yanzu haka ke samun yawaitar hadurran da ke da alaka da rakuma akan hanyoyin ta.
An bayyana cewa, rakuma wadanda suka saba kiwo da dare, suna tsallaka kan iyaka daga kasar Nijar zuwa cikin Nijeriya, suna yawo a sassan jihar Jigawa lamarin da ke haddasa hadurra da dama.