![]() |
Majalisar Dattawa |
Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan mafarauta-matafiya da aka yi a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Abdulaziz Yar’adua ya fitar a Abuja, ‘yan majalisar sun bayyana lamarin a matsayin abu ‘mai matukar tayar da hankali da bakin ciki.
A cewar sa mafarautan da suka tafi daga yankin Arewacin Nijeriya, an yi musu kisan gilla na wulakanci, na ba gaira ba dalili don haka sun yi Allah wadai da wannan danyen aikin, sun kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Edo da ta dauki matakin gaggawa domin zakulo batagarin da suka aikata wannan kisan tare da hukunta su.