![]() |
Bola Ahmed Tinubu |
An binne gawarwakin mutane 16 da suka rasa rayukansu a mummunan harin da aka kai musu a Jihar Edo.
Al’ummar Hausawa da abokan arziki, ne suka taru domin alhini da yin addu’o’i ga marigayan bayan yi musu Jana’iza tare da binne gawarwaki 16 a jihar ta Edo
Yayin da gwamnati ta ce tana bincike a kan kisan, kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na Addinai da sauran al’umma na ci gaba da yin Allah wadai da harin, tare da kiran lallai a hukunta wadan da suka yi aika aikar.