Wani makiyayi da shanunsa 12 sun bar duniya bayan da tsawa ta far musu a yankin Kudancin Kaduna.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin 4:30 na yammacin Lahadi, lokacin a kauyen Matuak Giwa, dake masarautar Moro’a a karamar hukumar Kaura ta Kaduna.
Hakimin garin Matuak Giwa, Simon Ayuba ya shaida wa Dailytrust cewa matashin makiyayin ya laɓe ne a lokacin da ruwa ke sauka tare da shanunsa a lokacin da lamarin ya faru.