![]() |
Natasha Akpoti |
Shugaban karamar hukumar Okehi a jihar Kogi, Amoka Monday, ya sanya dokar hana fita a fadin karamar hukumar, saboda matsalar tsaro biyo bayan hana tarukan siyasa da tarukan jama’a ba bisa ka’ida ba.
A cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa sanya dokar hana fita ya zama wajibi domin wanzar da zaman lafiya da kuma bin umarnin gwamnatin jihar Kogi da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, duk wanda aka samu yana taro ko kuma hada mutane ba tare da izini daga hukumomin da abin ya shafa ba za a kama shi kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.