![]() |
Bruno Fernandes |
Mai horar da kungiyar Manchester United Ruben Amorim ya shaida wa kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes cewa ba zai je ko’ina ba duk da rahotannin yiwuwar komawarsa Real Madrid.
Tauraron dan kasar Portugal mai shekaru 30, wanda ya zura kwallaye 95 a wasanni 277 tun bayan komawarsa daga Sporting Lisbon a shekarar 2020, yana da kwantiragi a Old Trafford har zuwa shekarar 2027.
Sai dai a kwanakin baya an alakanta Bruno da komawa kungiyar Real Madrid da ke kasar Spain.
Sai dai kocin kungiyar Manchester United Rubin Amorim ya ce yana da bukatar Bruno a kungiyar saboda suna son sake lashe gasar Premier, don haka don haka suna da bukatar ƙwararrun ‘yan wasa su ci gaba da kasancewa a Manchester United.