Dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa a shekarar 2023 Peter Obi, ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki masu amfani.
Obi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Arise News, ya soki matakin shugaba Tinubu ya dauka na barin naira tana tangal-tangal a kasuwar canjin kudade, da kuma kara ciyo basussukan ga kasar da sauran matsalolin tattalin arziki.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya tabbatar da cewa, da a ce shi ne shugaban kasa, da kasar ta ga sauye-sauye masu inganci a cikin shekaru biyu fiye da Shugaba Tinubu.