Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai Daniel Bwala, ya bayyana cewa har yanzu, dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na 2023 Peter Obi, bai murmure daga shan kayen da ya yi a lokacin zaben 2023.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Bwala ya ce kalaman Obi na baya bayan nan ba nazari da tunani a ciki.
Bwala’s yana mayar da martani ne ga hirar da Obi ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Talata inda ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.