Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Edo da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar Action Alliance da Dan takararta Adekunle Omoaje suka shigar kan zaben gwamna Monday Okpebholo da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, kotun mai alkalai uku ta yi fatali da karar, saboda rashin gamsassun hujjoji.
Jam’iyyar AA da Omoaje sun kalubalanci nasarar Okpebholo ya samu a zaben gwamna da aka yi a ranar 21 ga Satumba, 2024, bisa zargin rashin bin dokar zabe.