Masu gudanarwa da masu yada harkar zamba ta intanet wato Ponzi a Nijeriya na fuskantar barazanar hukuncin da bai gaza naira milyan 20 ba na tara ko kuma É—aurin shekaru 10 a gidan yari ba ko duka biyun.
Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkar kasuwar hannun jari, Sanata Osita Izunaso ne ya yi wannan gargadin a ranar Laraba.
Dan majalisar ya yi gargadin cewa biyo bayan sabuwar dokar da shugaba Tinubu ya amince da ita, zamanin yaudarar mutane ta hanyar saka hannun jari, saboda a yanzu hukumar kula da hada-hadar kudi ta Nijeriya SEC za ta rika kula da harkar kasuwancin crypto yadda ya kamata.