Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kafa kwamitin da zai bincike kan hatsaniyar da ta faru yayin da Sarki Muhammad Sanusi ke wucewa bayan gabatar da Sallar Idi, da kuma duk wani zargin take dokar hana yin hawan sallah da aka kafa a jihar.
Sanarwar da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar tace, an ɗora wa kwamitin mai mutum takwas alhakin gano musabbabin faruwar tashin hankalin da ya yi sanadin rayuwar wani ɗan vigilante ɗaya da jikkata wani mutum ɗaya.
Sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya umurci kwamitin ya bincike zargin taka dokar hana hawan sallah da aka yi kuma tuni aka gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi.