Daga wannan Laraba ce shugaban na Nijeriya zai tafi Faransa, inda zai kwashe wajen makonni biyu yana tattauna al‘amuran da za su bunkasa kasar, a cewar mai magana da yawunsa Bayo Onanuga
Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Tinubu zai ci gaba da kula da harkokin mulki daga can, inda zai rika magana da jami‘ansa kai tsaye.
Fadar shugaban kasar ta ce kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi ya sa asusun ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya kai dala biliyan 23.11 ya zuwa karshen shekarar 2024.