DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tinubu ya sauke Mele Kyari daga NNPCL

-

 

Engr. Bashir Bayo Ojulari ne zai ya maye gurbin Mele Kyarin da shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ayyana sauke shi daga shugabancin kamfanin man na NNPCL. 

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Nijeriya ta aike wa kafofin yada labarai ciki har da DCL Hausa, shugaban na Nijeriya ya kuma sauke Pius Akinyelure daga mukamin shugaban zartaswa na kamfanin man na NNPCL. 

Sanarwar wacce Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban kasa ya sanya wa hannu ta ce wannan mataki na sauke Mele Kyari zai fara aiki ne daga wannan Laraba 02 ga watan Afrilu. 

Haka kuma sanarwar ta yi karin bayani inda ta ce baya ga wadannan manyan jami’an kamfanin na NNPCL, shugaban na Nijeriya, ya sauke gaba daya mambobin kwamitin zartaswa na kamfanin NNPCL da aka nada su tare da Mele Kyari a watan Nuwambar 2023. 

Shugaban na Nijeirya ya nada Ahmadu Musa Kida daga jihar Borno don ya maye gurbin Pius Akinyelure a matsayin shugaban gudanarwa na kamfanin. 

Sanarwar ta fadar shugaban Nijeriya ta ambato sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na NNPCL da aka zabo daga yankuna shida na kasar, inda shugaba Tinubun ya nada Bello Rabiu domin ya wakilci shiyyar arewa maso yamma, sai Yusuf Usman daga shiyyar arewa maso gabas, Babs Omotowa daga arewa ta tsakiya

Shugaba Tinubu ya ce zartas da wadannan sauye-sauyen mukamai a NNPCL ya yi daidai da sashe na 59 na dokar bunkasa harkokin man fetur ta 2021 wacce ta ba shi damar daukar irin wannan mataki domin kyautata yadda ake tafiyar da harkokin man fetur da kuma bai wa masu zuba jari kwarin gwiwar shiga harkokin man fetur a Nijeriya. 

A karshen doguwar sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar cikin dare,  Bayo Onanuga ya ruwaito shugaba Tinubu na jinjina wa Mele Kyari da sauran jami’an da ya sauke daga mukamansu a NNPCL, musamman saboda yadda a cewar sanarwar, jagorancin Mele Kyarin dan jihar Borno ya taimaka wajen gyara matatun man fetur din da ke Fatakwal da kuma Warri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara