Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja CP Ajao Adewale ya jagoranci jami’an suka zagaya a titunan Garki da Lagos Street don tsaftace yankunan.
Wannan na zuwa ne don bikin murnar zagayowar ranar ‘yan sanda ta kasa ta shekarar 2025.
Bayanin hakan na kunshe a cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josephine Adeh ta aike wa DCL Hausa.