Hukumar zabe INEC ta ce Bukatar kiranye ga Sanatar Kogi ta Tsakiya ta gaza cika sharuddan da Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.
Idan za’a tuna, a baya bayan nan kimanin masu zabe dubu 250 daga mazabar Sanatar sun gabatarwa INEC takardun neman yi wa Sanatar kiranye, sakamakon zargin rashin girmama muradansu a wakilcin da take.