![]() |
Kashim Shettima |
Mataimakin shugaban kasar Shettima ya bar Abuja ne zuwa Dakar domin ya wakilci shugaba Tinubu a wajen bikin cikar Senegal shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Kasar Senegal na bikin ranar samun ‘yancin kai a ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, inda ake bikin ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960.
Ranar dai ta kasance cikin alfahari da al’ummar kasar, tare da shagulgula, da yin fareti da wasanni na al’adun kasar.
Halartar mataimakin shugaban kasa a taron na shekara-shekara, don girmama goron gayyatar da shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya biyo bayan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Senegal.