Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS za ta gudanar da taro a cikin watan Afrilun da muke domin tattaunawa kan harajin kashi 0.5 cikin 100 na shigo da kaya da kasashen yankin Sahel suka ƙaƙaba wa ƙasashen kungiyar ECOWAS a baya-bayan.
Shugaban sashen yaɗa labarai na Hukumar ECOWAS Joel Ahofodji, ya tabbatar da cewa majalisar kungiyar za ta yi taro a ranar 22 ga Afrilu don tattaunawa kan lamarin da sauran batutuwan da suka shafi kasashen, a cewar jaridar Dailytrust.
Da aka tambaye shi ko ECOWAS za ta dauki wani mataki na ramuwa dangane da harajin kashi 0.5 da AES suka sanya, Joel Ahofodji ya bayyana cewa, kungiyar za ta tattauna kan matakin da zata dauka a lokacin taron.