Gwamnatin Nijeriya ta amince da samar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko har 8,880 a fadin kasar.
A cewar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wannan na karkashin shirin sabuwar Nijeriya na shugaban kasa Bola Tunubu.
Kashim Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin kaddamar da cibiyar kula da cututtuka ta Sulaiman Adebola Adegunwa da aka samar a asibitin koyarwa ta jami’ar Olabisi Onabanjo (OOUTH) da ke Sagamu jihar Ogun.