![]() |
Peter Obi/Atiku Abubakar
|
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarSDP a zaben 2023, Adewole Adebayo ya ce manyan ‘yan siyasa ciki har da Atiku da Obi suna tattaunawa domin hada kai da jam’iyyar SDP, wadda a kwanakin baya tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki ya koma.
Da yake jawabi a gidan Talabijin na Channels TV a ranar Lahadi ya bayyana cewa suna maraba da mutanen da ke shiga jam’iyyar SDP.
Sai dai a cewarsa akwai wasu akwai matsalar da ake fuskanta da wasu ‘yan siyasa ke da fuska biyu, amma duk da haka suna maraba da duk wanda zai shiga cikin jam’iyyar su ta SDP.