Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Oluyemi Oluyede, ya kai ziyara zuwa karamar hukumar Bokkos a jihar Plateau, sakamakon harin ’yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 60.
Janar Oluyede ya jagoranci tawagar manyan hafsoshin soji domin duba irin barnar da aka yi, ciki har da asarar rayuka da lalata dukiyoyin al’umma.
Ana sa ran zai gana da shugabannin al’umma da na Fulani a yankin, tare da masu ruwa da tsaki, domin samun fahimtar juna da nemo hanyoyin magance rikice-rikice a yankin.